IQNA

Hadin Kan Al'ummar Musulmi Shi Ne Zai kawo Karshen 'Yan Takfiriyyah Na Daesh

19:10 - November 03, 2014
Lambar Labari: 1469965
Bangaren kasa da kasa, mataimakin shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na'im Kasim ya bayyana cewa dole ne al'ummar musulmi su hada kai domin fuskantar babban kalu bale ta'addancin Daesh, wadanda ke barazana ga kowa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Al-Nashrah cewa,  Hizbullahi ta kasar Lebanon ta daura alhakin duk wasu tashe-tashen hankulan da suke faruwa a kasashen Musulmi da na Larabawa a kan kasar Amurka.

A jawabinsa ga taron Taron Ba'alabak a makamar Sayyida Khaula diyar Sayyida Imam hussain (AS) da ke garin Sheikh Na’im Qasim mataimakin babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah a kasar ya jaddada cewar kasar Amurka ce ummul-haba’isin bullar duk wani tashe-tashen hankula a kasashen musulmi da na Larabawa, domin manufarta na kunna wutar rigingimu a kasashen ita ce kokarin mamaye dimbin arzikin kasashen tare da juya akalar harkokin cikin gidajen kasashen domin su yi daidai da masalaharta kuma koda cimma wannan buri nata zai kai ga hasarar rayuka da rusa kasashen.

Har ila yau Sheikh Na’im Qasim ya fayyace manufar Amurka da kawayenta na karfafa gwamnatin mamaya ta haramtacciyar kasar Isra’ila da cewa; kokari ne na firgita al’ummar Musulmi da na Larabawa a yankin gabas ta tsakiya domin mika kai ga munanan manufofin ‘yan mulkin mallaka masu girman kai na duniya.

1466634

Abubuwan Da Ya Shafa: Hezbullah
captcha