Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Al-alam cewa, shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah yayi kakkausar suka ga hare-haren da aka kai wa masu juyayin Ashura a kasashe daban-daban na duniya yana mai cewa yana mai cewa hakan wata alama ce ta rauni da gazawar da masu kafirta al’umma suke fuskanta a kokarinsu na hana al’ummar musulmi tunawa da Imam Husain (a.s).
Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a dazu-dazun nan a lokacin da yake gabatar da jawabin ranar Ashura da kungiyar ta shirya a birnin Beirut inda yayin da yake magana kan irin barazanar da masallacin Kudus yake fuskanta a halin yanzu daga wajen sahyoniyawan HKI, shugaban kungiyar ta Hizbullah ya kirayi gwamnatoci da kungiyoyin musulmi na kasa da kasa da kuma sauran al’ummar musulmi da su sauke nauyin da ke wuyansu na kare wannan masallaci mai alfarma.
Yayin da ya koma kan HKI da kuma barazanar da jami’anta suke ci gaba da yi na kawo wa kasar Labanon hari da nufin kawo karshen kungiyar ta Hizbullah, Sayyid Nasrallah ya ja kunnen sahyoniyawan da cewa matukar gigi ya debe su suka kawo wa Labanon hari to kuwa za su debi kashin su a hannu, don kuwa babu wani waje a cikin HKI da makamai masu linzamin kungiyar ba zai isa ba.
Dangane da kasar Siriya da kuma yakin da ke faruwa a can kuwa, Sayyid Nasrallah ya bayyana cewar da yardar Allah masu kafirta musulmi da suke yaki a Siriya za su sha kashi sannan kuma kasar Siriya za ta yi nasara kan wannan makirci da ake kulla mata
Rahotanni daga garuruwa daban-daban na Iran suna nuni da cewa tun da safiyar yau ne miliyoyin al’ummar kasar suka fito kan tituna don gudanar da jerin gwanon ranar Ashura da kuma ranar fada da ma’abota girman kan duniya.
Kamfanin dillancin labaran ya bayyana cewar tun da safiyar yau ne dubun dubatan daliban jami’oi da makarantun sakandare da tawagogi na addini masoya Imam Husaini (a.s) suka taru a gaban tsohon ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Tehran don raya ranar fada da girman kan duniya wacce ta yi daidai da ranar Ashura a wannan shekarar.
Rahotannin sun ce masu jerin gwanon dai suna rera taken Allah wadai da Amurka da HKI da sauran ma’abota girman kan duniya bugu da kari kan taken nuna so da kauna ga Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a).
Ranar Ashurar bana dai ta zo daidai da ranar 13 ga watan Aban, ranar fada da girman kan duniya don tunawa da ranar da daliban jami’ar Tehran mabiya tafarkin marigayi Imam Khumaini (r.a) suka kame ofishin jakadancin Amurka wanda ya zamanto cibiyar leken asirin Amurkan a Iran bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar.
1469981