Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na On Islam cewa, yahudawa masu tsatsauran ra'ayi na barazanar kona masallacin qods mai alfarma sakamakon abubuwan ad suke faruwa na boren palastinawa a birnin na qods.
Jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila tae da yahudawan masu tsatsauran ra'ayi na ci gaba da yin dauki ba dadi da matasan palastinawa a yankunan da ke gabacin birnin mai alfarma, rahotanni daga birnin na Qods sun ce 'yan sandan haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai samame a gidan mahaifan matasin nan Abdulrahamn Shaludi, wanda ya banke wasu yahudawa a birnin Qods da mota, inda ya kashe daya kuma ya jikkata wasu 8, kafin jami'an 'yan sanda su harbe shi, 'yan sandan na Isra'ila sun kame dan uwansa shakiki Izzuddin Shaludi da kuma wasu mutane a cikin danginsa.
Rahoton ya kara da cewa matasan apalastinawa suna ci gaba da yin dauki ba dadi tsakaninsu da jami'an tsaron yahudawan, wadanda ke amfani da harsasan roba da kuma masu rai gami da barkonon tsohuwa domin tarwata matasan masu bore, amma duk da haka har zuwa tsakar daren jiya ana bata kashi tsakanin bangarorin biyu a unguwannin da ke gabacin birnin Qods.
1471085