IQNA

A kasar Bahrain An Yi Allawadai Da Kisan Masu Taron Ashura A Ihsa

23:04 - November 11, 2014
Lambar Labari: 1472352
Bangaren kasa da kasa, dubban mutane sun gudanar da wata gagarumar zanga-zangar yin Allawadai a Bahrain kan kisan da aka yi fararen hula masu gudanar da tarukan Ashura a yankin Ihsa da k gabacin kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na babbar jam'iyyar adawa ta kasar Bahrain ta Al-wifaq cewa, a jiya ne dubban mutane suka gudanar da wani jerin gwano na yin Allawadai a Bahrain kan kisan da aka yi fararen hula masu gudanar da tarukan Ashura a yankin Ihsa da ke gabacin kasar Saudiyya tare da bayyana hakan da cewa aiki ne na dabbanci.
A cikin bayanin da masu gudanar da zanga-zangar suka fitar sun bayyana cewa wadanda suka aikata wannan mummunan aiki sun cancanci a gurfanar das u domin su fuskanci hukuncin day a dace sun a kisan dan adam, kuma mahukuntan kasar ta Saudiyya ne suke da alhakin daukar wannan mataki.
Haka nan kuma masu jerin gwanon sun bayyana cewa ya zama wajibia  dauki dukkanin matakai domin kare rayukan fararen hula masu gudanar da taruka daidai fahimtarsu da kuma akidarsu, tare da kwo karshen nuna wariya da tsangwamar da ake nunawa mabiya mazhabar ahlul baita  kasar ta Saudiyya, musamman a yankin gabacin kasar, wanda kuma a nan dukkanin arzikin kasar ta Saudiyya yake baki daya.
1471647

Abubuwan Da Ya Shafa: Barain
captcha