Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Los Angeles Times cewa, a yunkurin da gwamnatin Amurka take yi na kokarin jawo hankalin mabiya addinin muslunci a kasar domin samun yardarsu kan abubuwan da take aiwatar da ba su amince da su ba ta kirayi wani zama da hada bangarorin muslulmin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa bangaren kula da harkokin tsaro na majalisar dokokin kasar ne ya shirya wannan haduwa wadda ta samu halartar kimanin mutane 60 daga cikin jagororin mabiya addinin muslunci a kasar, wanda kuma sun saurari abin da jami’an na Amurka suka sanar da su na neman hadin kai domin gudanar da komai cikin fahimtar juna da kuma kare hakkokin musulmi.
Wadanda suka halarci taron sun koka ga jami’an naAmurka dangan eda abubuwa da dama da ake yi wa musulmi wadanda ba su dace ba, baya ga cin fuska da sukan fuskanta a wasu lokuta daga wasu marassa kamun kai, ita kanta gwamnatin Amurka tana matsa musu wajen aike musu da jami’an leken asiri da suke saka musu idoa kowane a lokaci a duk inda suke gudanar da harkokinsu na ibada da kuma daidaiku.
1473284