Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anadolu Agency cewa sakamakon ayyukan ta'addancin da 'yan takfiriyyah na Daesh ko kuma ISIS suke aikatawa a Iraki da Syria cin zarafin musulmi na karuwa a Birtaniya.
'Yan ta'addan suna aikata munanan ayyuka da sunan muslunci, wanda hakan ne ya bata sunan musulmi a kasar, inda wasu basa iya banbance cewa akwai musulmi wadanda su en suka fi yawa da ba su goyon bayan hakan.
Rundunar sojin kasar Iraki ta sanar da kammala tsarkake yankin Biji baki dayansa daga 'yan ta'addan takfiriyyah na ISIS da ke da'awar jihadi da suka yi wa wurin kawanya tun fiye da watanni uku da suka gabata.
A cikin bayanin da rundunar sojin kasar ta Iraki ta fitar a yau, ta tabbatar da cewa yankin Biji wanda a nan babbar matatar man fetur ta kasar take ya dawo karkashin ikon hukuma, bayan da 'yan ta'addan ISIS suka tsere sakakamon lugudan wuta daga suka sha daga sojin Iraki, bayanin ya ce an halaka 'yan ta'adda da dama, da suka fito daga kasashen dubniya daban-daban musamamn ma dai kasashen larabawa.
A jiya ma jami'an tsaron na Iraki sun sanar da kame wasu 'yan ta'addan na ISIS da suka fito daga kasashe sha bakawai akasarinsu 'yan kasashen ketare.