Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar presstv cewa a zaman da majalisar dokokin kasar Spain ta gudanar jiya ta amince da kasar palastinu mai cin gishin kanta.
Duk kuwa da cewa ‘yan majalisa 319 suka amince da hakan yayin da 2 rak kawai suka ki amincewa, amma dai hakan ya aike da wani sako a fili dangane da yadda al’ummomin duniya musamman a kasashen turai da suke mara baya ga dukaknin ayyukan ta’addancin Isra’ila ido suka fara dawowa ahalin yanzu suna juya mata baya.
Wata kotu ta musamman da ke bin kadun hakkokin bil adama da aka kafa kan keta hurumin dan adam da yahudawan sahyuniya ke yi a yankin Palastine, ta kirayi kotun manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hagu ta gudanar da bincike kan muggan laifukan da haramtacciyar kasar Isra'ila take aikatawa kan Palastinawa.
Kotun ta yi wannan kira ne a zaman da ta gudanar a birnin wanda aka kammala jiya Lahadi, inda ta yi bitar rahotanni da bayanai da ta harhada daga wakilanta masu sanya ido a Palastinu, da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, kan yadda haramtacciyar kasar Isra'la take cin zarafin Palastinawa da kuma aikata laifukan yaki a kansu, inda ta bukaci kotun manyan laifuka ta duniya da ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa karkashin kulawar majalisar dinkin duniya, domin ya gudanar da bincike kan wadannan laifuka.
1474919