Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na MA’A cewa, a jiya kungiyar palastinawa ta Hamas ta kirayi dukkanin mazauna yankunan gabar yamma da gabar kogin jodan da kuma sauran yankunan gabacin birnin quds da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin yin gangamin kare masallacin Quds mai alfarma a ranar juma a cikin wadannan yankuna.
Ana cikin halin zullumi a birnin Quds sakamakon tsauraran matakan da jami'an tsaron yahudawan Isra'ila suka dauka a birnin, bayan kiran da kungiyoyin gwagwarmaya suka yi kan gudanar da gangami da kuma bore a birnin da dukkanin biranan Palastinu.
Rahotanni daga birnin na Quds sun tabbatar da cewa jami'an tsaron sun kafa shingaye a dukkanin tituna musamman masu isa masallacin Quds mai alfarma, duk kuwa da cewa a yau palastinawa sun samu damar gudanar da sallar juma'a a cikin masallacin, lamarin da yahudawan suka haramta musu a makonnin da suka gabata.
A bangaren guda kuma jami'an leken asirin na yahudawan Isra'ila sun kame wasu mambobin kungiyar Hamas a birnin na Quds, bisa zarginsu da tattara bayanai kan yadda ministocin harkokin wajen Isra'ila Evegdor Liberman yake gudanar da harkokinsa, kama daga lokacin da yake fitowa daga gidansa, da kuma lokacin da yake isa ofishinsa, da kuma hanyoyin da yake bi.
1475490