IQNA

Dole A Mike Domin Banbance Ma Mutanen Musulunci Da Kuma Ta’addanci

20:14 - November 22, 2014
Lambar Labari: 1476066
Bangaren kasa da kasa, babban malami mai bayar da fatawa na kasar Masar Shuki Allam ya bayyana cewa ya zama wajibi kan malamai su mike domin banbanta musulunci da kuma ayyukan ta’addanci da ake aikatawa da sunansa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-wafd cewa, Shaki Allam babban malami mai bayar da fatawa na kasar Masar ya bayyana cewa ya zama wajibi kan malamai da sauran masana da su mike tsaye domin banbanta musulunci na hakika da kuma ayyukan ta’addanci da ake aikatawa da sunansa a duniya domin bata shi.
Babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa a kasar Masar Sheikh Shauqi Al-allam ya bayyana cewa kungiyar da ake kira Daular Musulunci a Iraki da Sham daesh gungu ne na 'yan ta'adda tantagarya da basu da wata dangantaka da addinin muslunci.

A cikin wani bayani da ofishin da ke a cibiyar drul ifta a birnin ya fitar a jiya shehin malamain ya ce 'yan ta'addan kungiyar daesh bai halasta ba a shar'ance a danganta su da addinin musulunci, domin dukkanin abin da suke yin a ta'addanci da sunan jihadi a cikin kasashen Syria da Iraki ya yi hannun riga da addinin muslunci da kuma koyarwar sunna irin ta manzon Allah.
Wannan babban malamin ya yi Allawadai da rusa kabrukan annabawa da salihan bayi gami da masallatai da majami'oi da 'yan kungiyar ta daesh suke yi yanzu ahak a cikin kasashen syria da iraki tare da muzantawa da kuma cin zarafin marassa rinjaye da suka mamaye yankunansu, musamman kiristoci da kuma izidawa da kuma sauran bangarori na musulmi a cikin wadannan kasashe.
1475828

Abubuwan Da Ya Shafa: Allam
captcha