IQNA

Za A Kafa Wata Cibiya Ta Hada Kan Mazhabobin Muslunci A masar

20:30 - November 22, 2014
Lambar Labari: 1476067
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin fitattun malaman addinin muslunci a babbar cibiyar muslunci ta Azhar da ke Masar y ace zai kafa cibiyar hada kan mazhabobin muslunci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na babbar cibiyar ahlul bait ta duniya cewa, Sheikh Ahmad Karimah daya daga cikin fitattun malaman addinin muslunci a bangaren shari’a a babbar cibiyar muslunci ta Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ya ce duk da matsin lamabar da yake fuskanta daga takfiriyawa, amma zai kafa cibiyar hada kan mazhabobin muslunci  a kasar domin samun hadin kai da fahimtar juna tsakanin musulmi.
A kwanakin baya ne dai sheikh Ahmad Karimah ya kawo ziyara birinin Qom na jamhuriyar muslunci ta Iran inda ya gana da manyan malamai da suka hada da Ayatollah Ozma Makarem Shirazi, da kuma wasu malaman da suka hada da na cibiyar ilimi ta biranin, ya kuma ziyarci hubbaren marigayi Ayatollah Ozma Borujardi.
Dangane da batun hadin kan musulmi jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa duk aiki da zai iya rururta wutar rikicin mazahaba a tsakanin shi’a da sunna, yana a matsayin yi wa Amurka da ‘yan sahayoniya hidima ne.
Jagoran juyin juya halin musuluncin wanda ya gana da bangarori daban-daban na al’ummar Iran a yau litinin ya yi ishara da kokarin da makiya su ke yi na raba addinin Musulunci da siyasa, da maida shi zama wani batu wanda ya shafi daidaikun mutane, sannan ya kara da cewa: Hakikanin abinda ya faru yana kore wannan tunanin na sakulanci domin kuwa yana tabbatar da matsayin Musulunci ne danagane da tafiyar da hukuma da kuma siyasa.
1475696

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha