Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Reauters cewa da dama daga cikin musulmin kasar Kenya sun nuna damuwa matuka a kan irin matakan da mahukuntan kasar suke dauka inda suke rufe masallatai a yankin Mobasa.
Musulmi a kasar Kenya sun bayana bacin ran su dangane da yadda ake rufe wasu masallatai a birnin Munbasa. A Makun da ya gabata ‘yan sanda a birnin Munbasa sun kai wani mumunan farmaki a wasu masalatai wadanda suka hada da masalatan Musa,Sakina, Mina da Safa sannan suka yi awan gaba da dariruwan Masallata da wannan Masalatai zan karkin yin zagon kasa ga tsoron kasa.
Har ila yau jami’an ‘yan sandar sun yi dawa’ar cewa sun kama makamai a cikin wadanda masallatai, zarkin da musulmin na kasar suka musanta, shugabanin musulmin a kasar sun nuna rashin amincewar su da take-taken Gwamnatin na cin zarafin Al’ummar musulmi a kasar ta Kenya da nufin yaki da ta’addanci.
A bangare guda ‘yan majalisun kasar ta Kenya sun bayyana damuwarsu da wannan mataki inda suka ce rufe masalatan da aka yi ba kan ka’ida ne ba, sannan sun bukaci Gwamnati da tagaggata kawo karshen wannan mataki.
1476164