IQNA

An bude cibiyar horar da masu tabligi musulmai a karon farko a kasar Brazil

Bangaren hulda ta kasa da kasa: An bude cibiyar horar da masu tabligi musulmai a karon farko a yankin Latine Amerika , a marecen jiya ne 15 ga watan Bahman aka bude a kasar Brazil.
A wani rahoto na cibiyar Alkur'ani da ke Iran Iqna bayan nakaltowa daga cibiyar watsa labarai ta Nasij,Abdul Baki Usman darektan zartarwa na cibiyar a yankin Latine Amerika kan haka ya kara da cewa: wannan cibiyar ilmantarwa ta addini ta fara ayyukanta a hukumce a bangaren horar da masu tabligi da masu wa'azi musulmai kuma sun fara ne a ranar 11 ga watan Isfad na wannan shekara.
Ya kara da cewa: musulmin kasashen Latine Amerika suna fama da karamcin masu Tabligi musulmi kuma a yanzu yawancin masu tabligi da ke yankin sun fit one daga kasashen musulmi da na larabawa da suma suke fama da matsalolin rashin iya yaren yin Magana da hulda da musulmin yankin.
Abdulbaki Usman ya yi tunatarwa da cewa: a halin yanzu sunada cibiyoyin musulunci 120 da kuma masallatai da guraren sallah masu yawa a Brazil sai dai yawancin wadannan masallatai da cibiyoyin musulunci suna fama da rashin mubaligai da masu wa'azi musulmai.

359261