Bangaren kasa da kasa: Jami'ar Al-azhar ta kasar Masar ta sanar cewa za ta bude wani sabon reshenta a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Mohit) cewa shugaban jami'ar Azhar (Sheikh Mohammad Sayyid Tantawi) ya bayyana cewa ya amince da neman da gwamnatin Sudan ta yi kan a bude wani sabon reshen jami'ar Azhar yankin Darfur, domin kuwa hakan na daya daga cikin irin ayyuka na kyautata danganataka da jami'ar take gunarwa tsakaninta da al'ummomin musulmi. Ya kara da cewa jami'ar ta gudar da ayyuka na horar da malaman addini da limamai da suka fito daga yankin Darfur na kasar Sudan kuma za ta ci gaba da yin hakan ta hanyar samara da wani reshen jami'ar a yankin.
367157