IQNA

Za A Gudanar Da Taron Bahasi Kan Wiliya A Birnin Tehran

Bangaren siyasa: A gobe ne idan Allah ya kai mu za a fara gudanar da taron bahasi kan wilaya da kuma mai tseratar da duniya na kasa da kasa a birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wata zantawa da ta hada shi da shugaban cibiyar da ke kula da bahasi kan wiliya da mai tseratarwa reshen lardin Azarbaijan da ke gabacin Iran Hojjatol island (Intezari) ya bayyana cewa za a gudanar da babban taron bahasi kan wiliya, wato wanda ya cancanci a jibinta masa lamari, da kuma wanda zai tseratar da al'ummar duniya, wanda akasarin addinai musamman wadanda aka safkar daga sama sun yi ammana kan cewa, wani zai zo a karshen duniya wanda zai tseratar da talikai daga barazanar da ke fuskantarsu, da kuma bala'oin da suka samu kansu a ciki, wanda addinai sun yi sabani kan hakinin ko wane ne, amma dai sun amince da samuwarsa da kuma zuwansa a karshen duniya.
Za a fara gudanar da taron ne daidai lokacin farawar imamancin Imam Mahdi (AS)

373619