Bangaren fasa: Shugaban gidajen radiyo na cikin gida da kuma daraktan radiyon da ke watsa shirye-shiryen matasa, sun ziyarciwasu daga cikin manyan malaman Iran da ake komawa zuwa gare su.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren kula da hulda jama'a na radiyon da ke watsa shirye-shirye don matasa cewa; Shugaban gidajen radiyo na cikin gida da kuma daraktan radiyon da ke watsa shirye-shiryen matasa, sun ziyarciwasu daga cikin manyan malaman Iran da ake komawa zuwa gare su, inda suka bayyana ma malaman irin ci gaban da harkar sadarwa take ci gaba da samu a Iran, musamman sabbin tashoshi da aka bude daga baya domin ilmantar da jama'a, musamman ma matasa daga cikinsu.
A nasa bangaren Ayatollah Makarim Shirazi, wanda daya ne daga cikin manyan malamai a Iran da ake komawa zuwa gare su, wanda kuma daya ne daga cikin wadanda tawagar ta kaima ziyara, ya yaba da irin kokarin da gidajen rayon Iran ke wajen wayar da kan al'umma tare da ilmantar da su.
375898