Bangaren fikra da ilimi: An gudanar da taron maulidin manzon Allah(SAW) a birnin Colombo na kasar Sri Lanka, taron da ya samu halartar dubban musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; an gudanar da taron maulidin manzon Allah(SAW) a birnin Colombo na kasar Sri Lanka, taron da ya samu halartar dubban musulmi. Jakadan Iran a kasar Sri Lanka (Rahimi) ya samu halartar taron, inda ya karanta wasu baitoci na yabon manzon Allah (SAW) daga nan kuma ya gabatar da jawabi kan muhimmancin gudanar da irin wadannan taruka da musulmi suke yi a sassa daban-daban na duniya, domin tunawa da wadannan ranaku masu albarka, tare dad a yin amfani wannan dama wajen yin kira zuwa hadin kai tsakaninsu. Ya ci gaba da cewa manzon Allah ya z one domin ya koyar da kyawan dabi’u tare da fitar da bil adama daga duhun jahilci zuwa ga haske shirya, kuma musulmi ba za su taba kasancewa masu biyayya ga manzo ba har sai sun yi koyi da shi a cikin wajen wakiltar addininsa da kyawawan dabi’u.
379040