IQNA

Girmama Makon Hadin Kai A Mazarussharif

Bangaren siyasa da zamantakewa:daruruwan yan Afganistan ne mazauna garin Mazarussharif suka halarci taron tuni da ranar haifuwar fiyayyan halitta (SWA) da jikansa Imam Ja'afar sadik (AS) domin girma makon hadin kan musulmi.
Daga afganistan cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: cibiyoyin addani ne suka shirya wannan gagaramin taro mai muhimmanci kan hadin kan musulmin duniya inda manyan malummai suka gabatar da jawabai da su kara kusanci tsakanin musulmi da shugabanninsu da malummanci da hakan zai bas u damar tunkarar makiyansu na ciki da waje masu kokarin rarraba masu kawuna.

378271