Bangaren siyasa da zamantakewa: Ayatollah Amini daya daga cikin limaman juma'a abirnin Qom ya bude wata hanya ta zantawa da matasa tare da ba su shawarwari ta hanyar internet.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da daya daga cikin shugabannin cibiyar ilimi ta Dar Alhadis da ke birnin Qom Mohamamd Rida Behrooz ya bayyana cewa; Ayatollah Amini daya daga cikin limaman juma'a abirnin Qom ya bude wata hanya ta zantawa da matasa tare da ba su shawarwari ta hanyar internet. Ya ci gaba da cewa bababr manufar samara da wannan hanya ita ce sawake ma matasa da suke neman shawarwari daga malamin dangane da lamurra da suka shafi zamantakewar rayuwarsu, ta yadda za ta yi daidai da koyarwar addinin musulunci. Ya ce ko shakka babu wannan hanya za ta taimaka ma matasan daga ko'in cikin fadin duniya domin samun shawarwari da za su dora su akn hanya, bisa la'akari da cewa sji matashi a kowane lokaci yana bukatar shawar da shiryarwa.
394083