IQNA

Shugaban Iran Ya Yi Nasara A Taron Birnin Jenneva

Bangaren siyasa da zamantakewa: Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad shi ne ya yi nasara a taron yaki da nuna wariya a birnin Jenneva.
Kamfanin dillancin labaran Ikan ya habarta cewa; a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a a birnin Zahidan na kasar Iran, Ayatollah Abbas Ali Sulaimani ya bayyana cewa; Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad shi ne ya yi nasara a taron yaki da nuna wariya da majalisar dinkin duniya ta shirya a birnin Jenneva na kasar Switzerland. Ya ci gaba da cewa a wajen taron shugaba Ahmadinejad yak are hakkokin al'ummar palastinu da ma sauran wadanda ake zalunta a duniya. Ya ce Ahmadinejad ya bayyana ma duniya cewa gwarzantaka day ace daga cikin al'adun Iraniyawa, kuma yadda al'ummomin duniya musamman ma wadanda ake zalunta daga cikinsu suka karbi wannan bayani tare da nuna farin cikinsu da gamsuwarsu da shi, ya tabbatar da cewa al'ummomin duniya sun fara dawowa daga rakiyar kasashe masu girman kai, sakamakon daurin gindin da suke baiwa Haramtacciyar Kasar Isra'ila.

393816