Bangaren rahoto: Sayyid Jafar Fatimi Nush Abadi ya bayyana cewa, bisa ga izinin da ma'aikatar kula da harkokin ilimi ta Iran ta bayar dangane da daukar dalibai Iraniyawa a jami'ar Al-mostafa, yanzu haka an fara dauakar dalibai Iraniyawa da suke son yin karatu a bangarori daban-daban da jami'ar ke bayar da ilimi kansu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga daya daga cikin jami'an jami'ar Al-mostafa da ke birnin Qom cewa; bisa ga izinin da ma'aikatar kula da harkokin ilimi ta Iran ta bayar dangane da daukar dalibai Iraniyawa a jami'ar Al-mostafa, yanzu haka an fara dauakar dalibai Iraniyawa da suke son yin karatu a bangarori daban-daban da jami'ar ke bayar da ilimi kansu. Daga cikin rassan da a halin yanzu aka fara rijistar dalibai da za su yi karatu a cikinsu kuwa har da bangaren nazari kan harkokin tattalin arziki, da ilimin sanin halayen jama'a, gami da ilmomin siyasa da zamantakewa, da kuma bangaren fikihu da shari'a, da ilimin hadisi da tafsirin kur'ani gami da kuma adabin larabci da kuma tarihin musulunci da dai sauran rassa da ake karatu a cikinsu a wannan jami'a.
411112