IQNA

Kafa Haramtacciyar Kasar Isra'ila Tunani Ne Na Bangaranci

18:03 - June 13, 2009
Lambar Labari: 1790422
Bangaren kasa da kasa; Wani malamin jami'a masanin tarihi a Amurka ya bayyana cewa; tunanin kafa haramtcciyar kasar Isra'ila tun farko ya samo asali ne daga tunanin bangaranci, da tunanin mamaye yankunan larabawa da cin zarafinsu da danne hakkon bil adama.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana na kasar Syria cewa; Wani malamin jami'a masanin tarihi a Amurka ya bayyana cewa; tunanin kafa haramtcciyar kasar Isra'ila tun farko ya samo asali ne daga tunanin bangaranci, da tunanin mamaye yankunan larabawa da cin zarafinsu da danne hakkon bil adama. Wannan fitaccen malamin jami'a da ya shahara a Amurka dangane da harkokin nazari kan batutuwa da suka shafi yankin gabas ta tsakiya, ya kara da cewa udawan sahyuniya da ke cikin Isra'ila akasarinsu suna da tunanin cewa ya kamata a kori sauran palastinawan da suka rage a yankunansu, tare da haramtawa masu gudun hijira dawowa gida.

419136



captcha