IQNA

15:31 - June 15, 2009
Lambar Labari: 1790740

An Fara Gudanar Da Taron Tattaunawa Tsakanin Sunna Da Shi'a A Birtaniya

Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da taron tattaunawa tsakanin sunna da shi'a a birnin London na kasar Birtaniya, wanda kuma wannan shi ne karo na uku da ake gudanar da irin wannan taro day a hada malamai daga dukkanin bangarorin biyu na 'yan sunna da kuma mabiya mazhabar shi'a.

Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Qods press cewa; An fara gudanar da taron tattaunawa tsakanin sunna da shi'a a birnin London na kasar Birtaniya, wanda kuma wannan shi ne karo na uku da ake gudanar da irin wannan taro day a hada malamai daga dukkanin bangarorin biyu na 'yan sunna da kuma mabiya mazhabar shi'a. Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin mahalarta taron masana ne da kuma malamai da suka fito daga kasashe daban-daban na musulmi da kuma na larabawa, daga cikinsu kuwa harm asana kan harkokin siyasar duniya. Babban dalilin day a jawo tattaunawar shi ne yadda wasu daga cikin malaman wahabiyawa suke fitar da fatawowin kafirta musulmi, musamman ma mabiya mazhabar shi'a.



419631
captcha