IQNA

An Fara Bayar Da Horon Karatun Kur'ani A Kasar Yeman

15:30 - June 15, 2009
Lambar Labari: 1790742
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani shiri na bayar da horo na lokacin bazaar a kasar Yeman, wanda ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta dauke nauyin shiryawa da gudanarwa a ko'ina cikin fadin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Yeman cewa; An fara gudanar da wani shiri na bayar da horo na lokacin bazaar a kasar Yeman, wanda ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta dauke nauyin shiryawa da gudanarwa a ko'ina cikin fadin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wannan shiri na bayar da horon karatun karatun kur'ani a fadin kasar shi ne, jawo hankulan matasa zuwa ga karatun kur'ani mai tsarki da kuma hardarsa, yanzu haka akwai cibiyoyi kimanin 319 da za su dauki nauyin gudanar da wannan shiri tare da hadin gwiwa da hukumar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Yeman.

419671


captcha