Bangaren kasa da kasa; Kasar Qazagistan za ta dauki nauyin bakuncin taron addinai da za a gudanar a cikin wata mai kamawa domin bahasi kan muhimman abubuwan da ya kamata addinai su riko da su wajen shiryatar da al'umma, tare da samun fahimtar juna tsakanin addinai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Saudi Gazete cewa; Kasar Qazagistan za ta dauki nauyin bakuncin taron addinai da za a gudanar a cikin wata mai kamawa domin bahasi kan muhimman abubuwan da ya kamata addinai su riko da su wajen shiryatar da al'umma, tare da samun fahimtar juna tsakanin addinai.Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar wakilai kimanin 600 daga kasashen sama da talatin da biyar, inda za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinai ta yadda za su zauna da juna lafiya baki daya.
421008