Bangaren kasa da kasa; Shugaban jam'iyar nan mai tsananin gaba da addinin musulunci a kasar Holland Geert Wilders ya yi kira da a fitar da dukkanin musulmi daga kasashen nahiyar turai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin sabah cewa; Shugaban jam'iyar nan mai tsananin gaba da addinin musulunci a kasar Holland Geert Wilders ya yi kira da a fitar da dukkanin musulmi daga kasashen nahiyar turai. Bayanin ya ci gaba da cewa Widers ya bayyana hakan ne a cikin wani bayani da ya gabatar a kasar Danmark a gaban taron fadin albarkacin baki da 'yancin bayani da aka gudanar a kasar. Taron ya samu halartar 'yan jarida daga kasashen turai da kuma na latin Amurka da kuma wasu kasashen nahiyar Asia. Geert y ace musulmi sun samu kutsawa cikin nahiyar turai kuma hakan na tattare da barana ga dukkanin al'ummomin turai, domin kuwa a cewarsa musulunci yana yin tasiri a cikin zukatan al'ummominsu fiye da sauran addinai.
421015