IQNA

Dan Majalisar Dokoki A Otrish Da Ya Ci Mutuncin Manzo (SWA) An Sake Hukumta Shi

Bangaren kasa da kasa: suzan Wintar dan majalisar dokoki a kasar Ostriya mai tsananin ra'ayi da a shekarar da ta gabata ya fuskanci hukumcin Kotu kan cin mutuncin Manzon rahama(SWA) an sake hukumta shi.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; Wintar da a shekarar da ta gabata ya yi maganganu da bayyana abubuwan cin mutunci da muzanta Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare da alayan gidansa da kuma abubuwa masu kima da daraja na addini da fuskantar hukumcin kotu ya kuma sake wata katobarar da sake fuskantar hukumcin kotu.


422396