Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da taron tattaunawa tsakanin addinai a birnin Dakar na kasar Senegal, wanda cibiyar kula da al'adu ta jami'ar Anta Diouf ta shirya gudanarwa, da nufin kara samar da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai na nahiyar Afirka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran APS cewa; An fara gudanar da taron tattaunawa tsakanin addinai a birnin Dakar na kasar Senegal, wanda cibiyar kula da al'adu ta jami'ar Anta Diouf ta shirya gudanarwa, da nufin kara samar da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai na nahiyar Afirka. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai mayar da hankali ne kan muhimman batutuwa da suke da danganataka harkokin addinin da al'adu na mabanbantan al'ummomi, da nufin samun fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinai da ke cikin nahiyar Afirka, kama daga musululmi da mabiya addinin kirista, har zuwa wasu kananan addinai marassa rinjaye a kasashensu.
424942