Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran turk time cew; An Fara gudanar da wani taro na kasa da kasa dangane da harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi a kasar Tataristan abirnin Qazan fadar mulkin kasar, wanda ke samun halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa tun kafin wannan lokacin ne aka shirya gudanar da zaman taron, amma saboda wasu dalilai aka dage shi zuwa wannan lokacin. Yanzu haka dai taron na samun halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da ma wasu kasashen da ba na musulmi ba, inda ake yin bahasi kan hanyoyin da ya kamata a bi wajen kafa habbaka tattalin azikin kasashen musulmi, haka nan kuma taron na samun halartar masana kimanin 600 dag kasashe sama da talatin.
425585