IQNA

Za A Gudanar Da Wani Zama Dangane Da Falalar Watan Ramadan

16:41 - June 29, 2009
Lambar Labari: 1796397
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da wani zaman taro, domin bayyana wa musulmi falalar da ke cikin watannin Rajab da sha'aban da kuma Ramadan, a Kossovo, inda za awayar da musulmin kasar dangane da muhimmancin gudanar da ayyukan ibada a cikin wadannan watanni masu alfarma.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Kossovo cewa; Za a fara gudanar da wani zaman taro, domin bayyana wa musulmi falalar da ke cikin watannin Rajab da sha'aban da kuma Ramadan, a Kossovo, inda za awayar da musulmin kasar dangane da muhimmancin gudanar da ayyukan ibada a cikin wadannan watanni masu alfarma. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar malaman yankin Balkan da suka hada da kasashen Bosnoya Solvakia da dai sauransu. A wajen taron za a yi bayani kan muhimmancin da ke tatatre da karatun kur'ani da kuna yawaita ibada, musamman ma a cikin watan Ramadan. Cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta yankin ita ce za ta dauki nauyn gudanar da zaman.

426415




captcha