IQNA

13:46 - July 28, 2009
Lambar Labari: 1806343
Bangaren kasa da kasa; An bude bangaren nazarin tauhi a cikin harshen turancin ingilishi a jami'ar Ankara da ke birnin Ankara na kasar Turkiya, wanda zai rika dauakar dalibai 'yan kasashen waje.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Yeni Asya na kasar Turkiya cewa; An bude bangaren nazarin tauhi a cikin harshen turancin ingilishi a jami'ar Ankara da ke birnin Ankara na kasar Turkiya, wanda zai rika dauakar dalibai 'yan kasashen waje , wanda kuma bangaren zai fara bayar da karatu a cikin watan farkon shekarar miladiyya mai kamawa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne karon farko da aka bude wani reshen nazarin tauhidi a jami'ar birnin Ankara da ma sauran jami'oin kasar Turkiya, wanda za a rika bayar da laccoci a cikin harshen turanci, wanda kuma zai rika daukar 'yan kasashen waje.

438302

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: