IQNA

An Gudanar Da taro Kan Tasirin Malaman Addini A Jabl Amil

Bangaren fikira da ilimi; An gudanar da wani taro kan tasirin malaman addinin musulunci a yankin Jabl Amil na kasar Labanan, wanda ya samu halartar malamai dam asana daga sassa daban-daban na kasar ta Labanan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga reshen yada labaransa na kasar Labanan cewa; An gudanar da wani taro kan tasirin malaman addinin musulunci a yankin Jabl Amil na kasar Labanan, wanda ya samu halartar malamai dam asana daga sassa daban-daban na kasar ta Labanan. Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da taron a ranar lahadi da ta gabata, inda aka gabatar da laccoci da nufin karfa musulmi mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da ma duk mai son jin tarihin Imam Hussain da yadda rayuwarsa ta kasance da sauran iyalan gidan manzon Allah SAW da suka rayu tare da shi a zamanin imamancinsa.

440172