IQNA

Hadin Kai Ne Ke Bada Tabbacin Kwaciyar Hankali Ga Duniyar Musulmi

Bangaren siyasa da zamantakewa: mai bada fatawa a Trablus na arewacin Labanon a cikin wani jawabi ya jaddada fadada hadin kai a tsakanin musulmi da hakan zai tabbatar da tsaro na hakika.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga Labanon ta watsa rahoton cewa: Malik Sha'ar a lokacin hudubar sallar karamar salla a masallacin Almansuri a Labanon ya bayyana cewa: bin umarnin Allah ba ita ce kawai hanyar yin ibadodi ana bukatar kyawawan dabi'u iya hulda da sauran mutane suma wasu nau'o'I ne na ibada. Idi yana nufin Akhalaki,hadin kai samara da kwaciyar hankali da sulhu a tsakanin al'umma da kuma kawar da duk wani bacin raid a gaba a tsakani ko kiyayya.

467546