Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban kasar na Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ya gabatar da jawabi a gaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a jiya da dare, ya yi nuni da hali mai hatsari da duniya ta ke ciki a wannan lokacin, sanann ya ce; maimakon yin magana akan yake-yake wajibi ne a yi tunani akan yadda za a shimfida zaman lafiya a duniya.
Shugaba Hassan Rauhani ya kuma yi ishara da takunkumin da aka kakabawa Iran wanda ba ya bisa doka, kuma ya ke a matsayin take hakkin bil’adama. Dangane da shirin makamashin Nukiliyar Iran kuwa, shugaban na Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ya sake jaddada cewa, hakki ne na dabi’a da doka na Iran.
Dr Hassan Rauhani ya kuma tabbatar da cewa amfani da makaman da su ke yi wa bil’adama kisan kiyashi ba ya cikin akdiar tsaro ta Iran, kuma mallakar tasu tana cin karo da koyarwa ta addini da kuma kyawawan halaye.
A wani sashe na jawabin nashi, shugaban kasar na Iran ya yi ishara da rashin gaskata juna da ke tsakanin kasarsa da Amurka sanann ya kara da cewa; Iran tana son ganin an kafa alaka ne bisa girmama juna da kuma maslahar da kasashe su ka yi tarayya akanta.
A wani labarin kuma, Yau ne alhamiss ake sa ran ministocin harkokin wajen kasashe biyar masu kujeru na din-din-din a comitin tsaro na majalisar dinkin duniya hadi da kasar Jamus zasu gana da takwaransu na jamhuriya misilimci ta Iran a birnin New York na kasar Amerika. Ministocin Kasashen biyar da suka hada da Amurka, Faransa, Rusha, Sin, da ingila hadi da kasar Jamus zasu gana ne da ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif akan shirin makamashin nukuliya na jamhuriya misilimci ta Iran da ake takadama akan shi.
Wanan ganawa da ministan harkokin wajen na wace ita ce ta farko da ministan harkikin wajen kasar Amurka John Kery ke halarta tareda sauran Ministocin kasashen ana sa ran zata haifarda da mai iddo idan akayi la'akari da jawabin shugaba Hassan Rohani a zauran taron MDD dake gudana a New York. Koda yake shugabar hulda da kasashen Turai Katerine Aston ta shaida cewa ganawar ta gajeran locaci ce ama da alamun zatayi tatsiri kuma zata share fagen wata ganawa da zasuyi da ministan harkokin wajen na Iran Zarif a watan October mai zuwa a Geneva.
1293480