Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na egynews cewa; An nuna wani fallen alkur'ani mai tsarki da rubutun wasu hadisan ma'aiki (SAW) da aka danganta da Imam Ali (AS) a birnin Bagdad na kasar Iraki. An nuna wannan rubutun kur'ani mai tsarki dad a hadisan ma'aiki ne a birnin Bagdada da nufin bayyana irin tarihin da addinin musulunci yake da shi.Yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da baje kolin kayan tarihin musulunci a birnin Bagadaza. 481906