Bangaren al'adu da fasaha; Za a fara gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan mahangar addinin musulunci da kuma harkokin sadarwa a birnin Qom da ke jamhuriyar musulunci ta Iran.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa dake birnin Qom cewa; Za a fara gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan mahangar addinin musulunci da kuma harkokin sadarwa a birnin Qom da ke jamhuriyar musulunci ta Iran. Bayanin ya ci gaba da cewa bababr manufar gudanar da wannan taro ita ce yin bahasi kan irin rawar day a kamata kafofin yada labarai su taka domin bayar da gudunmawa ga addi, da kuma kare addini daga farfagandar karairakin kafofin yada labarai na kasashe masu girman kai da ke hankoron bakanta surar addinin musulunci. 482123