IQNA

Limaman Juma'a A Beirut Na Gudanar Da Taro

Bangaren nazari da ilimi: Limaman masallacin juma'a a Beirut na gudanar da tarorruka a tsakaninsu.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; a wajen wannan taro da zama na malumman addini musamman limaman masallatai a birnin Beirut babban birnin kasar Labanon da aka gudanar a dakin taro na cibiyar darul ifta an samu halartar sheikh amin Alkurdi babban sakataren darul ifta'a da sheikh muhamma Jawidi shugaban ofishin da ke kula da harkokin addini a birnin Beirut.Limaman sun tattauna da nazari kan hanyoyin binkasa harkokin addini da kuma magance wasu matsalolin da ke addabar musulmi.

482034