IQNA

Ministan Al'adu Ya Kai Ziyara A Sashen Iqna A Baje Kolin Kayan Sadarwa

Bangaren fikira;Sayyid Mohammad Hosseini Ministan mai kula da harkokin al'adu na kasar Iran ya kai wata ziyara a sashen kamfanin dillancin labaran Iqna a baje kolin kayan sadarwa da ake gudanarwa a karo na goma sha shida.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Tehran cewa; Ministan mai kula da harkokin al'adu na kasar Iran ya kai wata ziyara a sashen kamfanin dillancin labaran Iqna a baje kolin kayan sadarwa da ake gudanarwa a karo na goma sha shida. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje kolin kayayyakin sadarwa na samun halartar kamfanonin yada labarai na cikin gida da wajen a jamhuriyar Musulunci ta Iran. Baje kolin zai kwashe tsawon mako guda ana gudanar da shi. 483667