Bangaren kasa da kasa; An sake buga wani littafi na cin zarafin addinin musulunci a kasar amurka, wanda ke dauke da hotunan batunci ga manzon Allah manzon Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; An sake buga wani littafi na cin zarafin addinin musulunci a kasar amurka, wanda ke dauke da hotunan batunci ga manzon Allah manzon Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka. Bayanin ya ci gaba da cewa littafin yana dauke ne da zane-zanen batunci irin wanda aka taba bugawa a kasar Danmark domin tsokanar musulmi ta hanyar yada zanen batunci ga manzon Allah tsirar allah da amincinsa su tabbata gare shi da iyalan gidansa tsarkaka. 493203