Bangaren al'adu da fasaha; An gudanar da wani taro kan goyon bayan Qods a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan, wanda ya samu halartar dubban mutane.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Jordan cewa; An gudanar da wani taro kan goyon bayan Qods a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan, wanda ya samu halartar dubban mutane. Bayanin ya ci gaba da cewa wadannan taruka na daya daga cikin tarukan da ake shiryawa domin nuna goyon baya ga al'ummar palastinu da kuma bayyana halin da suke ciki ga sauran al'ummomin duniya. 493221