Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar talabijin din Rasid cewa; Za a gudanar da tarukan shekara-shekara da aka saba gudanarwa a yankin Katif na mabiya mazhabar shi'a a kasar Saudiyya. Bayanin ya ci gaba da cewa mahukuntan wahabiyawa na Saudiyya sun dauki dukkanin matakan takurawa a kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsirar Allah da amincinsa su tabbata gare shi da iyalan gidansa da ke kasar, musamman ma a yankunan Katif. 494022