Bangaren al'adu da fasaha; An fara gudanar da wani zaman taro kan matsalolin da matasa musulmi suke fuskanta, wanda aka fara gudanarwa a birnin Makka mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Madina cewa; An fara gudanar da wani zaman taro kan matsalolin da matasa musulmi suke fuskanta, wanda aka fara gudanarwa a birnin Makka mai alfarma. Bayanin ya ci gab ada cewa an shirya gudanar da wannan taro ne domin yin bahasi kan irin matsalolin da suka kebanci matasan ne domin samar da dukkanin hanyoyi da suka dace domin shawo kan matsalolin. 496217