Aikin hajji, wani lokaci ne mai kyau na ababen da suke kusata mutum da Allah da kuma hasken tauhidi a fadin duniya; bukin hajji, wani idon ruwa ne da yake a fili da zai iya wanke alhaji daga daudar zunubi da gafala sannan kuma ya bude haske na fidira irin ta Ubangiji ga rai da zuciyarsa.
Watsi da tufafin alfahari da son nuna kai a mikatin hajji da kuma sanya tufafi iri guda mai launi guda na harami, wata alama ce da ke nuni da daidaituwa da kala guda na al'ummar musulmi da kuma nuni da hadin kai da kaunar juna da ke tsakanin musulmi a duk inda suke a duniya. Taken aikin hajj a wani bangare (daidai ya ke da fadin Allah Madaukakin Sarki cewa): Sa'an nan kuma abin bautawarku, Abin bautawa ne guda, sai ku sallama Masa. Kuma ka yi bushara ga masu kankantar da kai ne, a wani bangaren kuma (daidai ya ke da fadin Allah Madaukakin Sarki cewa): "Da masallaci mai alfarma wanda Muka sanya shi ga mutane alhali kuwa mazauni a ciki da bakauye daidai suke". Haka lamarin yake cewa Dakin Ka'aba, baya ga kasantuwarsa wakilin kalmar tauhid, haka nan kuma alama ce ta hadin kan kalmomi da ‘yan'uwantaka da kuma daidaito na Musulunci.
Musulman da suka taru a wannan wajen daga kusurwoyi hudu na duniya da shaukin yin dawafin Dakin Ka'aba da kuma ziyartar haramin Manzo mai girma, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa, wajibi ne su yi kokarin amfanuwa da wannan damar wajen karfafa irin alaka ta ‘yan'uwantaka da take tsakaninsu wanda magani ne ga da dama daga cikin manyan matsalolin da al'ummar musulmi suke fuskanta. A yau, a fili muke ganin yadda hannuwan masu fatan sharri ga duniyar musulmi, sama da shekarun da suka gabata, suke gudanar da ayyukan haifar da rarrabuwa tsakanin al'ummar musulmi. Hakan kuwa a daidai lokacin da al'ummar musulmi, sama da shekarun da suka gabata, suke bukatar hadin kai da kaunar juna a tsakaninsu. A fili ake ganin faratun makiya da suke jike da jini a dukkanin kasashen musulmi suna gudanar da danyen ayyukansu; (kasar) Palastinu tana karkashin mamayan yahudawan sahyoniya da kuma rayuwa cikin wahalhalu da matsaloli; masallacin Kudus (Al-Aksa) yana fuskantar gagarumar barazana; mutanen Gaza da ake zalunta bayan wannan kisan kiyashi maras tamka da suka fuskanta, har ila yau kuma suna cikin mafi mawuyacin hali; kasar Afghanistan tana cikin matsalar mamaya; a kowace rana suna fuskantar musibobi da matsaloli; rashin tsaro a kasar Iraki, ya kawar da kwanciyar hankali da rayuwar jin dadi daga al'ummar kasar; kisan gillan ‘yan'uwa da ke faruwa a kasar Yemen ya zamanto wata sabuwar matsala cikin zukatan al'ummar musulmi.
Kamata ya yi al'ummar musulmi a duk fadin duniya su yi tunanin cewa ya ya aka yi irin wadannan fitinu da yakukuwa, fashe-fashen bama-bamai da ayyukan ta'addanci da kisan gillan da suke faruwa a shekarun baya-bayan nan a kasashen Iraki, Afghanistan da Pakistan suke faruwa, sannan kuma daga ina ake tsara su da gudanar da su? Me ya sa a baya kafin shigowar sojojin mamaya na kasashen yammaci karkashin jagorancin Amurka wannan yankin al'umma ba sa ganin irin wadannan musibobi da matsaloli ba? A wani bangaren kuma ‘yan mamaya suna kiran kungiyoyin gwagwarmaya ta al'umma a kasashen Palastinu da Labanon da sauran yankuna daban-daban a matsayin kungiyoyin ta'addanci, sannan kuma a bangare guda suna tsarawa da kuma jagorantar ayyukan ta'addanci masu tsananin tada da hankali na kabilanci a tsakanin al'ummomin wannan yankin. Yankunan Gabas ta tsakiya da arewacin Afirka a lokaci mai tsawo sama da karni guda sun kasance cikin mulkin mallaka da mamaya da kwace musu albarkatun da suke da su da kuma wulakansu ta hannun gwamnatocin yammaci na Ingila da Faransa da sauransu kana kuma daga baya ta hannun gwamnatin Amurka; suna kwace musu albarkatun kasar da suke da su sannan kuma suka kawar da irin ruhin neman ‘yanci daga wajensu sannan kuma al'ummomin wadannan kasashe suka zamanto wadanda wadannan ‘yan kasashen waje suka yi garkuwa da su. Bayan da farkawa ta Musulunci da kuma irin gwagwarmayar al'ummomi suka bayyana, sai ya zamana ci gaban irin wannan yanayi (na mulkin mallaka) ya zamanto mai wahala ga azzaluman kasa da kasa sannan kuma batun shahada da tafiya zuwa ga Allah kuma saboda Allah har ila ya sake bayyana da kuma zama wani dalili wanda ba shi da makwafi a fagen jihadi na Musulunci, don haka masu wuce gona da iri sai suka koma ga wata hanyar ta daban da shigo da wani sabon tsari na mulkin mallaka don maye gurbin tsohon. Amma a yau fuskar shaidanci na mulkin mallaka, sun shigo fage da dukkan karfinsu domin dunkufar da Musulunci; kama daga amfani da karfin soji da bugu mai karfi da mamaya ta fili har zuwa ga bakaken hanyoyin farfagandarsu da kuma sauran dubban hanyoyi na yada kararraki da jita-jita, haka nan kuma kama daga shirya ayyukan ta'addanci da kisan gillan rashin imani har zuwa ga yada kayayyakin aiki na yada fasadi da yadawa da kwadaitar da (amfani) da muggan kwayoyi da lalata azama da ruhin kyawawan halaye na matasa, haka kuma kama daga kai hare-hare daga dukkan bangarori na siyasa a kan ciboyoyin gwagwarmaya har zuwa ga takalo fushi na kabilanci da kuma tsaurin ra'ayi na kungiyanci da haifar da kiyayya tsakanin ‘yan'uwa.
Matukar dai a tsakanin al'ummar musulmi da kuma tsakanin kungiyoyi da mazhabobi na Musulunci da kabilun musulmi suka samar da yanayin kauna da kyakkyawan zato da hadin kai a tsakaninsu da maye gurbin mummunan zato da mugun kallo wanda shi ne abin da makiya suke son gani da wadannan abubuwa, to kuwa za a iya magance wani bangare mai yawa na makirce-makirce da mummunan kulli (na makiya) sannan kuma mummunan makirci da kullinsu na gudanar da mulkin mallaka a kan al'ummar musulmi zai zamanto da mara ido.
Aikin hajji daya ne daga cikin mafi girman dama wajen cimma wannan manufa mai girma.
Al'ummar musulmi ta hanyar hadin kai da dogaro da tushe da asasin da suka yi tarayya a kansu da suka fito daga cikin Alkur'ani da sunnar (Ma'aiki) za su iya samun karfin da za su iya tsayin daka a gaban irin wannan shaidanci mai fuskoki daban-daban sannan su yi nasara a kansa da kuma tabbatar da imaninsu. Kasar Musulunci ta Iran ta hanyar koyi da darussan (Imam) Khumaini mai girma, (ta kasance) babbar misali ce da take a fili na irin wannan gwagwarmaya da ta yi nasara. Wadancan mutane sun sha kashi a kasar Musulunci ta Iran. Shekaru talatin na kafar ungulu da makirce-makirce da kiyayya kama daga kokarin juyin mulki da kallafaffen yaki na shekaru takwas, har zuwa ga takunkumi da kwace dukiya, haka nan kuma kama daga yaki irin na kwakwalwa da bakar farfaganda da amfani da kafafen watsa labarai (wajen yada kararraki) har zuwa ga kokari wajen hana ci gaba na ilimi da kuma samun ilmummuka na zamani ciki kuwa har da ilimi da fasahar nukiliya, kai hatta ma da tunzurawa da tsoma baki na fili cikin gagarumin zaben (shugaban kasa) na baya-bayan nan da aka gudanar, amma dukkanin wadannan abubuwa sun zamanto wani fage ne na shan kashin makiya, sannan kuma a wani karon ma wannan aya ta "Hakika kaidin Shaidan ya kasance mai rauni" ta sake bayyana a gaban idanun al'ummar Iran. A duk wani yanki na daban da aka samu irin wannan gwagwarmaya wacce ta ginu bisa asasin azama da imani wajen fuskantar ma'abota girman kai, to nasara tana tare da muminai sannan kuma rashin nasara da shan kashi wani sakamako ne da babu makawa cikinsa na azzalumai. Irin nasarar da aka samu a kasar Labanon cikin kwanaki 33 da kuma irin daukaka da nasarar Gaza cikin shekaru uku da suka gabata wata rayayyiyar shaida ce da take tabbatar da wannan hakika (ta taimakon muminai da shan kashin ma'abota girman kai).
Wasiyyar da nake jaddadawa (a ko da yaushe) ga dukkanin alhazan da suka sami wannan dacewa musamman ga malamai da masu wa'azin kasashen musulmi wadanda suka kasance a wannan waje na Ubangiji da kuma limaman juma'a na wadannan haramomi guda biyu masu girma (Makka da Madina); ita ce cewa su san irin nauyin da ke wuyansu a yau wanda kuma ake bukatarsa cikin gaggawa ta hanyar kyakkyawar fahimtar wannan lamari. Su sanar da masu saurarensu da dukkan karfinsu irin makircin makiya Musulunci sannan kuma su kirayi al'umma zuwa ga hadin kai da kaunar juna. Lalle su nesanci duk wani abin da zai haifar da mummunan zato tsakanin musulmi a tsakaninsu sannan kuma duk wani take (da la'ana) da suke da ita su watsa ta a kan ma'abota girman kai da makiya al'ummar musulmi da iyayengijin dukkanin fitina wato yahudawan sahyoniya da kasar Amurka. Sannan kuma su bayyanar da barranta daga mushirikai cikin maganganu da ayyukansu.
Cikin kaskantar da kai na ke rokon shiriya da nasara da taimako da rahamar Allah Madaukakin Sarki a gare ni da kuma dukkaninku baki daya.
Wassalamu alaikum.
Sayyid Ali Husaini Khamene'i
3, ga watan Zul Hajj al-Haram 1430 (Hijiriyya)
21, Nuwamba, 2009 (Miladiyya)
http://hausa.khamenei.ir/