IQNA

14:58 - December 07, 2009
Lambar Labari: 1858018

'Yan Shi'a A Turkiya Sun Bukaci Hutun Ghadir A hukumance

Bangaren kasa da kasa; mabiya mazhabar shi'a na kasar Turkiya sun bukaci a hutu a hukumace a ranakun idin ghadir, domin samun damar gudanar da bukukuwansu kamar yadda ya kamata.

Kamfanin dillancin labaran kasar Turkiya ya habarta cewa; daya daga cikin jagororin mabiya mazhabar shi'a na kasar Turkiya Ali Yearal kuma shugaban cibiyar bunkasa al'adu da ilimin Musulunci a kasar ya sanar cewa; mabiya mazhabar shi'a na kasar Turkiya sun bukaci a hutu a hukumace a ranakun idin ghadir, domin samun damar gudanar da bukukuwansu kamar yadda ya kamata. 504513
captcha