Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar talabijin din palastinu ta PNN cewa; An gudanar da wani zaman taro kan mu'ujizar kur'ani mai tsarki wanda manyan malaman jami'a asuka gudanar a jami'ar Khan Yunus da ke yankin Zirin Gaza.
Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya yi dubi kan muhimman batutuwa da suka danganci matsayin kur'ani da kuma hikimomin da ke tattare a cikin kalamnsa gami da gajiyarwa wadda ke birbishin tunanin dan adama. 506064