Bangaren harkokin kur'ani : sabon bugo na talatin da hudu na mujjalar wata wata ta Arijul Kur'ani a kasar Labanon ta fito da hadin guiwar kungiyoyin kur'ani na wannan kasa ke daukan nauyin fitowa da buga ta.
Daga reshenta da ke Labanon cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; sabon bugo na talatin da hudu na mujjalar wata wata ta Arijul Kur'ani a kasar Labanon ta fito da hadin guiwar kungiyoyin kur'ani na wannan kasa ke daukan nauyin fitowa da buga ta.Wannan fitowar ta musamman ce ta watan Sha'aban shekara ta dubu daya da dari hudu da talatin da daya hijira kamariya kuma ta kumshi bayanai da bahasoshi masu yawa na kur'ani mai girma.
620858