IQNA

14:20 - September 06, 2010
Lambar Labari: 1988719
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani baje koli na kayayyakin abincin halal a kasar Rasha, wanda babban kwamitin malaman addinin Musulunci na kasar tare da hadin gwiwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar za su shirya gudanarwa.Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na kwamitin malaman addinin muslunci na kasar Rasha cewa, za a gudanar da wani baje koli na kayayyakin abincin halal a kasar Rasha, wanda babban kwamitin malaman addinin Musulunci na kasar tare da hadin gwiwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar za su shirya gudanarwa a cikin shekara mai kamawa.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Andreh Denisov ya aike da wata wasika zuwa bababn sakataren kwamitin malaman addinin Musulunci na kasar Rasha, inda a cikin wasikar ya bayyana jin dadinsa da wannan shiri, ya kuma tabbatar da gamsuwar ministan harkokin wajen Rasha da hakan.

648344
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: