IQNA

An Tarjama Littafin Muhammad Rasulollah (SAW) Da Harshen Jamusanci

Bangaren fikira da ilimi, An tarjama littafin nan da ke bayani kan rayuwa da tarihin manzon Allah (SAW) a cikin harshen jamusanci, wanda cibiyar buga littafai ta Isfor a tsibirin Cyprus ta dauki nauki nauyi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren kula da hulda da jama'a na cibiyar al'adu an bayyana cewa, an tarjama littafin nan da ke bayani kan rayuwa da tarihin manzon Allah (SAW) a cikin harshen jamusanci, wanda cibiyar buga littafai ta Isfor a tsibirin Cyprus ta dauki nauki nauyi.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan littafi yana daya daga cikin littafan da aka tarjama a cikin harsuna daban-daban domin bayyana hakikanin tarihin manzon Allah (SAW) da kuma rayuwarsa ga sauran al'ummomi.

A cikin littafin an kawo tarihin rayuwar ma'aiki bisa dogaro da wasu daga cikin littafan da aka rubuta a cikin harsunan larabci da kuma turkanci.

Mujalladi na farko daga cikin littafin ya kawo bayani dangane da tarihin annabawa daga farko har zuwa Annabi Isa (AS) a sauran kuma tarihin ma'aiki.

664845