Bangaen kasa da kasa, Za a gudanar da maulidin Imam Rida (AS) a birin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, tare da halartar malamai na mabiya mazhabar shi'a da kuma malaman sunna.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na zainabiyya an habarta cewa, za a gudanar da maulidin Imam Rida (AS) a birin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, tare da halartar malamai na mabiya mazhabar shi'a da kuma malaman sunna daga sassa daban-daban na birnin.
Bayanin ya ci gaba da cewa irin wadannan taruka na maulidin limaman gidan manzon Allah (SAW) da kuma lokutan shahdarsu na daga cikin muhimamn taruka da mabiya mazhabar iyalan gidan manzo ke gudanarwa a Turkiya.
Yanzu haka dai an kammala dukaknin shirye-shirye na gudanar da wannan babban taro a babbar cibiyar mabiya mazhabar iyakan gidan manzon Allah da ke birnin na Istanbul.
676875