IQNA

An Kammala Shirin Bayan Da Horon Koyon Farisanci A Istanbul

Bangaren fikira da ilimi, An kammala wani shiri na bayar da horo kan koyon harshen farisanci da aka gudanar a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, wandaaka gudanar a babban ginin cibiyar marubuta ta kasar.


Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki na Iqna ya habarta cewa, an kammala wani shiri na bayar da horo kan koyon harshen farisanci da aka gudanar a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, wandaaka gudanar a babban ginin cibiyar marubuta ta kasar ta Turkiya.

Wanann rahoto ya yi nuni da cewa wannan dai ba shi karo na farko da aka gudanar da irin wannan shiri na bayar da horon ba, amma kuma shirin na bana ya sha bnban da makamantansa da aka gudanar a shekarun da suka gabata.

Babban jami'i mai kula da ofishin bunkasa harkokin al'adu na Iran a kasar Turkiya ya bayyana cewa, babbar manufar gudanarda wannan shiri dai ita ce kara fadada dangantaka ta al'adu tsakanin kasashen biyu.

676072