Bangaren kasa da kasa; taron mata a Musulunci da ofishin da ke kula da yada al'adun Jamhuriyar Musulunci a Iran ya shirya a Kudu maso gabacin Asiya kuma wannan taro an gudanar da shi ne a dakin taro na ofishin jakadancin Iran da ke birnin Kalalampur fadar mulkin kasar Malaisiya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; taron mata a Musulunci da ofishin da ke kula da yada al'adun Jamhuriyar Musulunci a Iran ya shirya a Kudu maso gabacin Asiya kuma wannan taro an gudanar da shi ne a dakin taro na ofishin jakadancin Iran da ke birnin Kalalampur fadar mulkin kasar Malaisiya. A lokacin gudanar da wannan taro an tabo matsalolin da ke addabar mata da kuma hanyoyin da za a magance su irin matsalolin da suke fama da su.
680425